Hukumar EFCC ta ci alwashin daukan tsatstsauran mataki akan duk dan siyasar data kama da laifin siyan kuri'a, tare da bayar da kyautar kudi ga duk Wanda ya fallasa mai bayar da cin hanci a ranar Zabe

<

Yayin da babban zaben shugaban kasa ke kara karatowa, wanda za'a gudanar a ranar Asabar, Hukumar EFCC ta yi barazanar kama duk wani dan siyasa da ke yunkurin sayen kuri'ar zabe a kowane É“angare na kasar nan.

Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya fada cikin wata sanarwa da aka bayar a Vanguard a ranar Laraba, ya sanar da 'yan Nijeriya cewa duk wanda ya bada rahoto akan wani dan siyasa da yaga yana sayen kuri'a a ranar Zane to yanada lada mai tsoka. da za su ba da gudummawa ga masu saye ko karfafawa da sayen kuri'un zabe a lokacin zaben.

Kodayake shugaban bai bayyana yawan kudin da zasu biya ga dukan Wanda ya fallasa masu sayen kuri'ar ba, Magu ya bayyana cewa, da wadanda ke siyan kuru'un, da kuma wadanda ke siyar da kuru'un, dukkaninsu masulaifi ne a duk inda aka kama su. . "

"Muna so mu gargadi 'yan Najeriya daga wadanda suke son su yaudari masu jefa kuri'a,"sannan ya kara da cewa, "Har ila yau, akwai dokokin da ke cikin Dokar Zabe, 2010 (EA), da ke hana yaudarar masu jefa kuri'a.

Wanne siddabaru yan siyaysa suke yiwa yan Nigeria? 

"Don kaucewa shakku, Sashi na 124 na Dokar Zabe, 2010, ya ce duk wanda ya biya kudi ga kowa, a matsayin cin hanci a kowane zabe, ya cancanci aci tararsa kudi Naira dubu 500 ko kuma dauri a kurkuku na tswon wata 12 ko duka biyu. 

"Sashe na 124 na Dokar Zabe 2010, ya kuma bayyana cewa, duk wanda ya karbi kudi ko kyauta don jefa kuri'a ko a bashi kudi domin a hana shi yin zabe, to za aci tarar shi Naira dubu 500 ko wata 12 a kurkuku ko biyu.

"Saboda haka, muna roÆ™on 'yan Najeriya su fita daga harkar yan siyasa masu cin hanci da kuma jefa kuri'a ga 'yan takarar da suka cancanta. 

"Har ila yau, muna amfani da wannan dama, don bayyana cewa, EFCC, tare da haÉ—in gwiwar INEC, za ta biya duk wani wanda ya ba da cikakken bayani akan wani dan siyasa da yaga yana bada cin hanci da rashawa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.