FADAKARWA: Akan bindige barayin akwati; daga comrade Isma'il Auwal

<


Naga anata yamutsa hazo akan Maganar da shugaban Kasa Muhammad Buhari yayi cewa duk wanda ya saci akwatin zabe Abakin rayuwar Shi. Masoyansa na kareshi, yan adawarsa na kushe Wannan ra'ayin.

Yana daya daga cikin dalilan dayasa na zabi zama kan katanga, saboda hakane zai bani 'yancin fadar abinda nake ganin dai dai ne ko akasin haka akan kowane irin yanayi.

Akwai irin mutan da duk abinda ya fito daga bakin Dan jam'iyyar adawa to a gurinsu wannan kuskure ne, haka kuma idan dan jam'iyyarsu ko kuma ubangidansu na siyasa yace waccen abu kaza bakine sai suce bakine kirin, daga cikinsu kuma harda wanda nake tunanin matakin iliminsu da shekarunsu bai kamata ya barsu su fito a wannan rukunin mutanen ba, kamata ace su fitila ne ga al'umma, ba kuma sajin tsoron fadin abinda ya bayyana gaskiyane abisa haske na ilimi batare dasan ko kuma bangarenci ba.

Ba masanin doka bane ni, amma zanso ace komawa mukayi mukaga abinda kundin dokokin Nigeria yace akan irin wadannan mutane da suke aikata irin wannan laifin, idan cewa abindige, to inatare da shugaban Kasa, dukda cewa akwatin zabe ko kusa darajarsa batakai ran Mutum ba. idan kuma akasin hakane ina banranta kaina daga wannan matakin.

Inama ace yanda shugaban kasa yayi Magana akan Barayin akwatina cikin baccin rai da fushi, haka yayi akan mutanen dake tada hankula a zamfara, dakuma barayin mutanen da suke jahar Katsina.

Ina kuma kira ga Mutane da mutuna cewa soyyaya itace idan jagoranka yayi kuskure ka nuna masa kuskurensa, mukuma tuna cewa cigaban kasarmu Nigeria yafi bukatar jam'iyyarka, ko kuma Dan Takararka shi kadai.

Inama zamu dinga tunawa da kasarmu a farko kafin jam'iyar siyasarmu, inama zamu daina kallon bambamcin jam'iyya muna zabar wanda ta bayyana yanada manufofi, inama duk zamu hawo katanga muyita tura Shugabannin mu har sai sun magance mana matsalolin da suka addabi kasarmu Nigeria.

Ismail Auwal
Daga kan katanga

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.