Kafin A Zubar Da Jinin A Jahar Sokkoto : Jan hankali da sheikh Ja'afar Mahamud Adam yayi

<


Kafin rasuwar Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam (Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa) ya sha jan hankalin hukumomin tsaro akan fitinar jihar Borno, aka yi biris ba tare da daukar mataki ba. Har yanzu Najeriya na dandana kudarta akan wannan fitina.
Jaridar Vangurd ta taba yin wani rahoto akan yadda ake hada baki da ‘yansanda ana dillancin bindigo a jihar Zamfara, rashin daukar mataki akan lokaci yau ga jihar ta zama Kabari-Salamu-Alaikum.
Rahotanni na ta yawo a kafar sada zumunta da jaridu na wasu bakin-haure da suka yada zango a jihar Sakkwato dauke da manyan makamai. Suna yi kira ga mutane da su bi tsarin da suka zo musu da shi.
Yin biris da wannan rahoton ba tare da binciken sahihancin sa ba, babban sakaci ne gami da sakarcin mahukuntan kasa. A bincika a kuma dauki matakin gaggawa tun kafin wankin hula ya kai mu yin dare.
Na tabbatar da yau rahoton sirri aka samu za a kai hari Abuja, da tuni an dauki matakin gaggawa. Kamar yadda da rahoton kai wa Tambuwal hari ko Wammako aka samu da tuni an dauki mataki. Don haka a gaggauta daukar matakin kare rayukan talakawan jihar Sakkwato ko domin sake zaben ku a Gwamna da Sanata.
Wani abin ban haushi da matasan Sakkwatawan shine yadda suka rika bi duk titin da Tambuwal ya bi suna sharewa saboda ya bar APC ya koma PDP amma a halin yanzu sun kasa yin ayari zuwa gidan Sarkin Musulmi ko Majalisar jiha ko gidan Gwamnati domin kira a bincika wannan batu.
Kamar yadda suka kasa amfani da kafafen sadarwa na zamani domin kaddamar da kiraye-kiraye ga ‘yan Majalisar wakilai na tarayya da Sanatocin su akan su kai kukan su ga hukumomin tsaron kasa a bincika wannan batu gami da daukar mataki.
Yau abin Allah Ya kiyaye idan fitinar ta zo ‘ya’yan Talakawa ne za su fi kowa shan azaba. Ku duba abinda ya ke faruwa a jihar Zamfara. Ku tashi ku ja hankalin ‘yan siyasar Ku yanzu ba wannan ne matsalar su ba, ba a jihar Sakkwato suke da zama ba. Matsalar su a halin yanzu KURI’UN Ku a zabe mai gabatowa.
Shin a jihar Zamfara kun ga ko kun ji ana Garkuwa ko kashe ‘ya’yan Manya. Ganin Buzu a Masallaci ya isa darasi ga Tunkiya.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.