Hukumar INEC ta bayyana lokacin da na'urar tantance masu kada kuri'a wato card reader zata dauke a ranar zabe!

<


Mahmood Yakubu, shugaban Hukumar INEC, ya bayyana wannan a cikin wani jawabi na manema labaru game da ci gaban da hukumar ta samu wanda akayi a Abuja ranar Laraba.

Shugaban hukumar INEC ya ce an sake dai-dai ta na'urar tantance katin zaben.

"An tsara kowacce card reader dinnen domin mazabu daban daban kuma za'a bude su don amfani a karfe 8 na ranar zaben, sannan a rufe su ta atomatik da karfe 10 na dare, "inji shi.

"Jiya, na bayar da rahoton kashi 95 cikin 100 na kammala aikin. Ina farin cikin bayar da rahoto cewa yanzu mun sami kashi 100 cikin 100 na kammala. Muna da kyau mu ci gaba da wannan kira. "

Yakubu ya kara da cewa hukumar zabe ta cigaba da kokari. Ya bayyana cewa an tura kayan aiki a duk jihohi na fadin kasarnan da kuma babban birnin tarayya (FCT) wato abuja.

Har ila yau, ya kara da cewa, jihohin 10 sun riga sun fara raba kayan aikin zuwa kananan hukomomi yayin da wasu jihohi suma zasu yi haka kuma za su gama a ranar Alhamis.

Kasashen da ya lissafa sun hada da Adamawa, Anambra, Benue, Ekiti, Jigawa, Katsina, Ogun, Osun, Oyo, da Taraba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.