An bukaci da a dakatar da dan wasa Bale daga buga wasanni

<

Shuwagabannin gasar La Liga sun bukaci hukumar kwallon kafa ta Spaniya (RFEF) da ta hukunta dan wasaGareth Bale, sakamakon irin yadda ya yi murnar cin kwallo a karawa da Atletico Madrid.

Bale dan kwallon tawagar Wales ya yi nuni da hannayensa a murnar kwallo na uku da ya ci wa Real Madrid kuma na 100 jumulla, wanda hakan ya harzuka magoya bayan Atletico.

Bale din ya yi wata alama da hannuwansa, wadda batanci ce a Spaniya, kuma hakan ne ya harzuka magoya bayan Atletico Madrid.

Cikin hukuncin da La Liga ke sa ran a dauka kan dan wasa Bale ya hada da dakatarwa daga buga wasa hudu zuwa wasa shabiyu.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.