Boko Haram: ISWAP ta saki mata 2 bayan harin data kaiwa gwamnan jahar Borno

<

The Islamic State in West African Province, wato ISWAP, kungiyar tarayyar duniya ta Boko Haram ta sako 'yan mata biyu daga cikin wadanda aka kama a lokacin da aka kaiwa gwamnan Jihar Borno hari akan hanyar Dikwa da Gamboru Ngala ranar 12 ga Fabrairu, 2019.

Wadannan mata biyu, wadanda aka ce sun sake fitowa ranar Lahadi, sun zo tare da sako daga 'yan ta'adda cewa sauran matan da suke hannunsu, za suyi aure dasu a ranar Alhamis.

Matan da suka shiga babban birnin jihar a ranar Litinin tare da sakon yan kungiyar Boko Haram, sun ce kungiyar tana da mayaka masu yawa, matasa da kuma tsofaffi kuma suna kula da yankin dake tsakanin Dikwa da Gamboru-Ngala a jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

Hukumar zabe INEC ta yanke shawarar sake dawo da yakin neman zabe wato kamfen

"Akwai da yawa daga cikin mu mata, maza, matasa da kuma na tsakiya. 'Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin maza da matasan da suka dauka. A ranar Jumma'a ne suka nemi mu biyu da mutafi gida. Sunnan suka nuna mana hanyar da za mu biyo kuma suka umarce mu da muyi bayanin sakon su zuwa ga hukumomi cewa a ranar Alhamis za su aure sauran matan dake wajensu, "Daya daga cikin matan da suka bayyana kanta a matsayin Fatima sun shaida wa DAILY POST cewa

Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a Arewa maso Gabas, tare da wani harin da aka kai a Gajigana, a arewacin Borno da Buni Yadi a Jihar Yobe.

Kungiyar ta yi zargin cewa mutane 42 ne suka rasa rayukansu, da kuma sace mata da dama a lokacin harin da aka kai a gwamnonin Jihar Borno, amma gwamnati ta musanta hakan, inda ta ce kawai mutane uku ne aka kashe yayin da aka kai harin.


Tushen labari:

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.